logo

HAUSA

CMG Ya Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Ofishin Kula Da Kafofin Yada Labaru Na Al’umma Na Argentina

2022-02-07 20:58:11 CRI

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da ofishin kula da kafofin yada labaru na al’umma na kasar Argentina.

Yayin da shugaban Argentina Alberto Fernández ke halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing ke gudanarwa da wasu harkoki masu ruwa da tsaki, shugaban CMG kuma babban editan CMG Shen Haixiong, da Valeria Zapesochny, shugabar ofishin suka sanya hannu a madadin sassan biyu.

Bayan tattaunawa, sassan biyu za su aiwatar da hadin gwiwa a fannonin shirye-shirye, da fasahohin watsa labarai, da musayar ma’aikata, da taimakawa juna a fannonin bisa daidaito, da martaba juna, da zantawa bisa abota, da nufin kara bunkasa musaya, da koyi daga juna, da musaya tsakanin al’ummu, da bude sabon babin hadin gwiwar Sin da Argentina daga dukkanin fannoni.  (Saminu)

Saminu