logo

HAUSA

Shugaban babban zauren MDD: wasannin Olympics na Beijing na da muhimmanci ga hadin kan duniya

2022-02-04 20:28:25 CMG

Shugaban babban zauren MDD: wasannin Olympics na Beijing na da muhimmanci ga hadin kan duniya_fororder_0204-UNGA-Faeza

Shugaban babban zauren MDD na 76, Abdulla Shahid, Ya ce wasanni Olympics na Beijing zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kan duniya da farfadowa daga ammobar COVID-19.

Abdulla Shahid ya fadawa Xinhua cewa, wasannin za su taimaka wajen bayyana juriyar bil adama da hadin kai da yunkurin neman farin ciki, yayin da ake fuskantar rashin tabbas da annobar COVID-19 ta haifar. (Fa’iza Mustapha)

Faeza