logo

HAUSA

Shugaba Xi ya yi jawabi a wurin liyafar maraba ta gasar Olympics ta Beijing

2022-02-05 20:32:25 CMG

Shugaba Xi ya yi jawabi a wurin liyafar maraba ta gasar Olympics ta Beijing_fororder_0205-Xi-speech-Ibrahim

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi a wata liyafa da aka shirya a babban dakin taron jama'a da ke birnin Beijing, fadar mulkin kasar Asabar din nan, domin maraba da manyan baki na kasa da kasa da suka halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing na shekarar 2022.

Xi ya bayyana cewa, za mu tuna da ainihin burin gasar Olympics, da tabbatar da zaman lafiya a duniya tare.  Za mu inganta ruhin wasannin Olympics, da tinkarar kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta ta hanyar yin hadin gwiwa. Za kuma mu yi aiki tare bisa manufar harkokin Olympics da ci gaba da martaba ci gaban bil-adama.(Ibrahim)

Ibrahim