logo

HAUSA

An kammala taron koli karo na 35 na kungiyar AU

2022-02-07 19:54:32 CRI

A jiya Lahadi ne aka kammala taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU, karo na 35 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, taron da ya hallara shugabannin kasashen Afirka mambobin kungiyar, bisa taken "Gina tsari mai karko, na samar da abinci mai gina jiki a nahiyar, da gaggauta gina al’umma, da bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin Afirka. An kuma yi amfani da taro na wannan karo, wajen fayyace muhimman burikan Afirka na bana, da ma shekaru na gaba.

Taron na yini biyu, wanda ya gudana a bana, bayan gamuwa da cikas a bara sakamakon bazuwar cutar COVID-19, ya samu kiraye kiraye, na bukatar ci gaba da hadin kan Afirka, ta fuskar yaki da annobar COVID-19. Kaza lika an bukaci mahalartansa, da su gaggauta magance kalubalen yawaitar juyin mulki ba bisa ka’ida ba, da kuma mummunan tasirin ayyukan ta’adanci dake addabar sassan nahiyar.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, wanda a bana ya karbi jagorancin kungiyar ta AU na karba-karba, daga shugaba Felix Tshisekedi na jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, ya jaddada bukatar kara azama, wajen shawo kan kalubalen rashin tabbas da sassan Afirka ke fuskanta, da matsalar sauyin yanayi, da kuma mummunan tasirin da annobar COVID-19 ke haifarwa al’ummun Afirka.

Shugaba Sall ya kara da yin kira ga hadin kan Afirka, ta yadda za a kai ga cimma nasarar muradun nahiyar na shekaru 50, wato zuwa nan da shekarar 2063.    (Saminu)

Saminu