logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da juyin mulkin da bai yi nasara ba a Guinea-Bissau

2022-02-03 16:33:44 CMG

Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da juyin mulkin da bai yi nasara ba a Guinea-Bissau_fororder_0203-Buhari-Ibrahim

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, jiya Laraba ya tattauna da takwaransa na kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ta wayar tarho, inda ya yi Allah-wadai da yunkurin da aka yi a ranar Talatar da ta gabata, na ruguza kundin tsarin mulkin da aka kafa a kasar da ke yammacin Afirka.

Shugaba Buhari ya ce, yana fatan yin aiki tare da Embalo, domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da karewa da inganta tsarin demokuradiyya da kimarta a fadin yankin, da ma nahiyar Afirka baki daya.

Ya kuma yabawa dakarun da ke biyayya ga kasar Guinea-Bissau, kan yadda suka nuna kishin kasa wanda ya kai ga gagarumar nasara a kan sojojin da ba su da da’a.

Embalo ya tabbatar wa Buhari cewa, an shawo kan al’amura a Guinea-Bissau kuma komai ya daidaita yadda ya kamata.(Ibrahim)

Ibrahim