logo

HAUSA

Wanda ake zargi da kona ginin majalisar dokokin Afirka ta kudu ya yi amfani da takardu da fetur in ji masu gabatar da kara

2022-01-31 16:59:32 CMG

Wanda ake zargi da kona ginin majalisar dokokin Afirka ta kudu ya yi amfani da takardu da fetur in ji masu gabatar da kara_fororder_0131-S.A.-Saminu

Wata sanarwa da sashen gabatar da kara a Afirka ta kudu ko NPA ya fitar, ta bayyana yadda mutumin da ake zargi da tada gobara, a ginin majalissar dokokin kasar ya kunna wuta ta hanyar amfani da wasu takardu, da kwali da wani fetur da ya shiga da shi a cikin kwalba.

Sanarwar ta ce, wanda ake zargin mai suna Zandile Christmas Mafe, ya karya kofar ginin majalissar, ya kuma jima kadan a cikin ginin, kafin ya kunna wutar da ta yi matukar lalata sassan ginin.

An dai gabatar da wadannan bayanai ne a ranar Asabar, gaban kotun dake sauraron karar da aka shigar game da Mafe, yayin da lauyoyin sa suka bukaci a ba da shi beli, ko daya yake, nan take lauyoyin dake gabatar da kara sun soki bukatar ba da belin. Idan har an same shi da laifi, zai iya fuskantar daurin rai da rai a gidan gyaran hali.

Mr. Mafe mai shekaru 49 da haihuwa, na fuskantar tuhumar karya kofa domin aikata ta’addanci, da barnata dukiya da sata. To sai dai kuma ya musanta aikata laifukan da ake zargin sa da su, ko da yake masu gabatar da kara sun mikawa kotu takardun shaidar amincewarsa da aikata laifukan lokacin da ake tuhumarsa.

Masu gabatar da karar sun ce, Mafe ya yi ikirarin aikata wannan ta’asa ne da nufin tilasawa shugaban kasar mai ci Cyril Ramaphosa sauka daga mukamin sa nan take, da kuma bukatar a saki Janus Waluz, mutumin da aka yankewa hukuncin dauri, bayan da kotu ta same shi da laifin kisan tsohon shugaban jam’iyyar Kwaminis ta kasar Mr. Chris Hani, a shekarar 1993.    (Saminu)

Saminu