logo

HAUSA

Kakakin gwamnatin Guinea-Bissau ya ce masu yunkurin juyin mulki ba su yi nasara ba

2022-02-02 17:20:49 CMG

Kakakin gwamnatin Guinea-Bissau ya ce masu yunkurin juyin mulki ba su yi nasara ba_fororder_0202-Guinea-Saminu~1

Kakakin gwamnatin Guinea-Bissau Pamela Ferreira, ya ce sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar ba su yi nasara ba. Mr. Ferreira wanda ya bayyana hakan a daren jiya Talata, ya ce wasu sojoji masu bore sun yi yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Umaro Sissoco Embalo, amma kuma hakan su bai cimma ruwa ba.

Shugaba Umaro Sissoco Embalo, na tsaka da jagorantar taron ministoci a fadar gwamnati da yammacin Talata, lokacin da sojojin suka afka musu da harbin kai mai uba da wabi da manyan makamai, lamarin da ya sabbaba rasuwar da dama daga masu tsaron lafiyar shugaban.   (Saminu)

Saminu