Gwamnatin Najeriya ta kawo karshen dakatarwar da ta yiwa Twitter na tsawon watanni 7
2022-01-13 20:38:34 CMG
Gwamnatin Najeriya ta kawo karshen dakatarwar da ta yi wa shafin sada zumunta na Twitter, watanni bakwai bayan da ta dakatar da gudanar da ayyukan kamfanin da ke Amurka, a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.
Babban darektan hukumar fasahar sadarwa ta kasar Kashifu Abdullahi, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, dage haramcin da aka yiwa kamfanin a Najeriya zai fara aiki ne daga karfe 12 na safiyar yau Alhamis agogon kasar, bayan da kamfanin ya amince da cika dukkanin sharuddan da gwamnatin Najeriya ta gindaya masa.(Ibrahim)