logo

HAUSA

Sin Ta Samar Da Karin Gudunmawar Riga-kafin COVID-19 Ga Zanzibar Ta Tanzania

2022-01-30 17:23:39 CRI

A ranar Juma’a Zanzibar ta kasar Tanzania ta sake karbar alluran riga-kafin COVID-19 200,000 na kamfanin Sinopharm, wanda kasar Sin ta samar.

Zhang Zhisheng, babban jakada a karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Zanzibar ya mika alluran ne ga wakilin gwamnatin Zanzibar, kana ministan ilmi da koyar da sana’oi, Simai Mohammed Said, a filin jirgin saman kasa da kasa na Abeid Amani Karume.

Jami’in ya yabawa taimakon da kasar Sin ta samar, ya ce, alluran za su taimaka wajen yi wa al’ummar Zanzibar allurar riga-kafin cutar ta COVID-19.

Ministan ya kuma bukaci dukkan al’ummar Zanzibar da su karbi riga-kafin cutar ta COVID-19, inda ya ce, alluran suna da inganci matuka bayan samun amincewar hukumar lafiya ta duniya WHO.

Zhang ya jaddada aniyar kasar Sin ta taimakawa al’ummar Zanzibar a koda yaushe, a kokarin yaki da annobar COVID-19.

A ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2021, Zanzibar ta kasar Tanzania ta karbi rukunin farko na riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinovac gami da alluran sirinji wanda kasar Sin ta bayar a matsayin gudunmawa.(Ahmad)

Ahmad