logo

HAUSA

Shugabannin Afrika sun yi kira da a tabbatar da adalci wajen rabon riga kafin COVID-19

2021-09-25 17:05:49 CRI

An tabo batun riga kafin COVID-19 yayin babban taron MDD, inda shugabannin Afrika suka koka game da karancinsu a yankin, suna kira da a samar da alluran cikin adalci.

Shugaban Namibia Hage Geingob ya bayyana wa taron cewa, rashin daidaito a fannin rabon riga kafin ya kai a kira shi da nuna wariya.  

Ya ce abun takaici ne yadda a wasu kasashe ake wani mataki na yi wa jama’a riga kafin a zagaye na 3, yayin da a wasu kasashen, jama’a da dama ke jiran karbar allurar a zagaye na farko.

Ita ma a jawabinta karo na farko a babban taron MDD, shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, wadda ta bayyana rashin daidaiton a matsayin abu mai muni, ta yi kira ga kasashen dake da rarar riga kafin, su raba su ga kasashe masu bukata.

A nasa bangaren, shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa wanda ya yi jawabi ta kafar bidiyo, cewa ya yi, ta hanyar hadin kai da goyon bayan juna ne aka samu kayayyakin kiwon lafiya yayin barkewar cutar a bara, yana mai cewa wajibi ne kasashen duniya su tabbatar da dorewar wadannan ka’idoji wajen samar da riga kafin cikin adalci. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha