logo

HAUSA

Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Tabbatar Da Samar Da Alluran Rigakafi A Yammacin Afirka Da Sahel

2022-01-11 20:16:41 CRI

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira da a tabbatar da cewa, an samar da alluran rigakafi ga kasashen yammacin Afirka da yankin Sahel.

Dai Bing ya shaida wa taron kwamitin sulhu na MDD kan ofishin kula da yammacin Afirka da yankin Sahel cewa, a kwanan nan an samu karuwar masu dauke da cutar COVID-19 a kasashen yammacin Afirka, kuma halin da ake ciki bai ba da damar yin kyakkyawan fata ba, kana saurin yaduwar nau’in COVID-19 na Omicron, ya nuna rashin daidaito game da yadda ake raba alluran rigakafin.

Don haka, wakilin na kasar Sin ya ce, ya zama dole a ci gaba da tallafawa kasashen yankin don yakar cutar, da kara ba da taimako, da samar da hanyoyin samar da lafiya, da samun alluran rigakafi cikin sauki, da yayata cire batun hakkin mallakar fasaha kan alluran rigakafin ga kasashen yankin da kuma tallafawa wajen samar da alluran rigakafin a cikin kasashen

Wakilin ya jaddada cewa, kasar Sin za ta aiwatar da sakamakon babban taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kara ba da taimako wajen yaki da cutar a yankin.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya