logo

HAUSA

WHO ta kaddamar da manyan tsare-tsaren yiwa al’umma rigakafin COVID-19 a duniya

2021-10-08 13:42:19 CRI

A ranar 7 ga wata, Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban magatakardan hukumar kiwon lafiyar duniya WHO ya sanar da kaddamar da manyan tsare-tsaren yiwa al’umma rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, a kokarin ganin an yiwa al’ummar kasa da kasa da yawansu ya kai kashi 40% alluran kafin zuwa karshen wannan shekara.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, yanzu an yi alluran da yawansu ya wuce biliyan 6.4 a duniya, yayin da yawan mutanen da aka kammala yi musu allurar duka ya kai sulusin jimillar yawan mutanen duniya. Amma yawan alluran da kasashe masu karancin kudin shiga suka samu bai kai 0.5% bisa jimillar alluran duniya ba, yayin da yawan mutanen da aka kammala yi musu allurar duka a Afirka bai kai kashi 5% ba bisa jimillar yawan mutanen nahiyar. A cewarsa, hukumar WHO ta kaddamar da manyan tsare-tsaren yiwa al’umma rigakafin cutar COVID-19 nan da tsakiyar shekarar 2022, a kokarin ganin an yiwa al’ummar kasa da kasa da yawansu ya kai 40% allurar kafin zuwa karshen wannan shekarar, kana nan da tsakiyar shekarar 2022 za a kammala yiwa al’ummar da yawansu ya kai kashi 70%. Za a bukaci alluran da yawansu ya kai biliyan 11 domin cimma wannan manufa, lamarin da zai danganta da batun raba allurar, a maimakon samar da allurar.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen da suka yi wa yawancin al’umma allurar da su yi musayar ajandar mika allurar tare karkashin shirin COVAX da asusun ajiya na amintattu na Afirka kan sayen allurar rigakafin COVID-19, tare da cika alkawarinsu na raba allurar. Ya kuma yi kira ga kamfanonin samar da allurar da su ba da fifiko kan yin la’akari da kuma aiwatar da kwagilolin da suka daddale da shirin COVAX da asusun ajiya na amintattu na Afirka kan sayen allurar rigakafin COVID-19, ta yadda dukkan sassan duniya za su kyautata kwarewarsu ta samar da allurar. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan