logo

HAUSA

Shugaban Zanzibar Na Tanzaniya: Likitocin Kasar Sin Sun Daga Matsayin Kiwon Lafiya A Wurin

2021-09-04 17:05:55 CRI

Shugaban Zanzibar na kasar Tanzaniya, Hussein Ali Mwinyi ya ziyarci asibitin Abdulla Mzee, wanda ya fi girma a tsibirin Pembam, inda ya gana da tawagar ma’aikatan lafiyar kasar Sin karo na 30, wadda ke ba da taimako a asibitin. Tawagar da ta fito daga lardin Jiangsu na kasar Sin.  

Hussein Ali Mwinyi ya shaidawa likitocin cewa, kasar Sin ta dade tana taimakawa Zanzibar, inda zuwa yanzu, ta tura tawagar ma’aikatan lafiya sau 30, wadanda suka gudanar da ayyuka yadda ya kamata, tare da ceton rayukan mazauna wurin, da kiwon lafiyar jama’ar Zanzibar, da kuma daga matsayin aikin kiwon lafiya a wurin matuka. Don haka ya jinjina musu sosai.  

Mwinyi ya ci gaba da cewa, yanzu tawagar karo na 30 za ta kammala aikinta ba da dadewa, inda zata koma kasar Sin. Don haka ya roki mambobinta da su mika godiyarsu ga gwamnatin kasar Sin da iyalansu. Shugaban ya kuma yabawa dukkan ayyukan da suka yi a Zanzibar. Ya kuma yi fatan cewa, zumuncin da ke tsakanin Sin da Tanzaniya da kuma Sin da Zanzibar, ba zai kare ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan