logo

HAUSA

AfCFTA da abokan hulda sun kaddamar da tsarin biyan kudade a tsakanin kasashen don bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen Afrika

2022-01-14 10:56:23 CRI

AfCFTA da abokan hulda sun kaddamar da tsarin biyan kudade a tsakanin kasashen don bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen Afrika_fororder_220114-A1-Afrika

Sakateriyar yarjejeniyar ciniki maras shinge na kasashen Afrika (AfCFTA), da bankin shigi da fici na Afrika (Afrexim), da sauran abokan hulda sun kaddamar da wani tsarin biyan kudade na kasashen Afrika wato (PAPSS), a ranar Alhamis, da nufin bunkasa kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika.

Matakin ya biyo bayan wata gagarumar nasara ce da aka samu a wani gwajin da aka gudanar na tsarin biyan kadade a kasashe shida na yammacin Afrika da suka hada da Ghana, Najeriya, Gambia, Liberia, Guinea, da Saliyo.

Yayin kaddamar da shirin, mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia ya ce, tsarin na PAPSS zai kawo karshen dogaron da kasashen Afrika ke yi na biyan kudade daga bangare na uku wajen biyan kudaden cinikayya a nahiyar, kana zai taimaka wajen karfafa cinikayya da bunkasa masana’antu da samar da dawwamamman ci gaba da bunkasa ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afrika. (Ahmad)