logo

HAUSA

Kungiyar injiniyoyin Afrika ta goyi bayan aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA

2021-10-09 17:06:26 CMG

Kungiyar injiniyoyin Afrika ta goyi bayan aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA_fororder_1009-AfCFTA-Ahmad

Kungiyar injiyoyin kasashen Afrika (FAEO), a ranar Juma’a ta bayyana goyon bayanta na aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci marar shinge ta Afrika (AfCFTA), domin ba da damar bunkasa hada hadar cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar.

Kudirin amincewar wanda kungiyar FAEO ta zartar bayan kammala taron kolinta na kwanaki biyar, ta bayyana cewa, rawar da injiniyoyi ke takawa yana da muhimmanci wajen tabbatar da cimma muradun yarjejeniyar AfCFTA, da ajadan bunkasa Afrika ta AU nan da shekarar 2063, da kuma muradin samar da dawwamamman cigaba.

Bisa ga wadannan dalilai, kungiyar ta ce, za ta bi dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar da kulla kyakkyawar alaka da yarjejeniyar AfCFTA, da AU, da kuma gwamnatocin dukkan kasashen Afrika.

Sanarwar ta ce za su cigaba da yin cudanya da sakatariyar AfCFTA, da shugabannin mambobin kasashen, domin taimakawa wajen gina muhimman kayayyakin more rayuwa da ake bukata don cimma nasarar kafa tsarin kasuwanci marar shinge a tsakanin dukkan kasashen Afrika.(Ahmad)

Ahmad