logo

HAUSA

EAC ta kusa kammala shirin gabatar da tanadin haraji mai nasaba da yarjejeniyar AfCFTA

2021-11-18 10:21:30 CRI

EAC ta kusa kammala shirin gabatar da tanadin haraji mai nasaba da yarjejeniyar AfCFTA_fororder_s01-EAC bloc nears conclusion of tariff offer to conform to AfCFTA tariffs

Kungiyar raya gabashin Afirka ta EAC, ta dukufa wajen cika sharuddan ta na shiga a dama da ita, a yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA a takaice, inda a yanzu haka EACn ke tsara yanayin harajin da kasashe mambobinta za su gabatar karkashin yarjejeniyar.

Wata sanarwar da ofishin EACn ya fitar a jiya Laraba a birnin Arushan kasar Tanzania, ta nuna cewa, an mika alhakin tsara harajin ne ga ofishin kungiyar mai lura da cinikayya, hada hadar kudi da zuba jari ko SCTIFI a takaice, wanda zai kira taron kwararru kan batun a ranar 15 ga watan Disamban dake tafe.

Sanarwar ta kara da cewa, an umarci sakatariyar EAC da ta yi nazari kan alkaluman karin harajin da kasashe mambobin kungiyar suka gabatar a matakai daban daban.

Da yake karin haske kan hakan, babban sakataren EAC Peter Mathuki, ya ce akwai tarin ayyuka da suka wajaba a gudanar, don aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA yadda ya kamata.

Kasashen nahiyar Afirka sun kaddamar da fara aiki da yarjejeniyar  AfCFTA tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021, kuma yarjejeniyar za ta shafi al’ummun nahiyar su kimanin biliyan 1.3, ciki har da al’ummun kasashe mambobin EAC da suka hada da Burundi, da Kenya, da Sudan ta kudu, da Rwanda, da Tanzania da Uganda. (Saminu)