logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Najeriya ya yi kira da a bunkasa fadakarwa domin ci gajiyar yarjejeniyar AfCFTA

2021-07-28 11:05:36 CRI

Mataimakin shugaban Najeriya ya yi kira da a bunkasa fadakarwa domin ci gajiyar yarjejeniyar AfCFTA_fororder_210728-s04-nijjeriya

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya yi kira da a bunkasa fadakar da masu gudanar da mafi kankanta, da kanana, da matsakaitan sana’o’i, game da alfanun yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar Afirka ko AfCFTA a takaice.

Yemi Osinbajo, wanda ya yi kiran a jiya Talata, yayin taron yini biyu, don gane da tasirin yarjejeniyar ta AfCFTA a birnin Abuja. Ya ce masu sana’o’i mafi kankanta, da kanana da matsakaita na bukatar cikakkiyar fadakarwa game da moriyar dake tattare da wannan yarjejeniya.

Mataimakin shugaban Najeriya ya ce wani rahoton baya bayan nan da aka fitar, bayan tuntubar wannan rukuni na masu sana’o’i su 1,800 a kasar. Ya nuna cewa mafi yawan su, musamman masu kananan sana’o’i, ba su ma san da wannan yarjejeniya ta AfCFTA ba. Don haka ya bukaci a kara azama, wajen wayar da kan wannan rukuni na masu sana’o’i, ta yadda za su kasance cikin shirin ci gajiya, daga tanadin dake cikin yarjejeniyar.

Osinbajo ya ce, AfCFTA na da damammaki na bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afirka, ana kuma fatan za ta samar da hadaddiyar kasuwar nahiyar mai mutane biliyan 1.27, da GDPn da zai kai dalar Amurka tiriliyan 3.4.   (Saminu)