logo

HAUSA

Bangaren Jigilar Kayayyaki Cikin Jirgin Sama Na Kasar Sin Ya Farfado Zuwa Matakin Kusa Da Na Shekarar 2019

2022-01-12 19:42:46 CRI

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin CAAC, ta sanar Larabar nan cewa, sashen jigilar kayayyaki cikin jirgin sama na kasar ya farfado zuwa kusa da matakin da yake a shekarar 2019.

Jami'ar hukumar ta CAAC Xu Qing ta shaidawa manema labarai cewa, ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan jigilar dakon kaya cikin jirgin sama a kasar ya karu da kashi 8.2 bisa dari daga shekarar da ta gabata, zuwa tan miliyan 7.32, wanda hakan ya kai kashi 97.2 cikin 100 na adadin a shekarar 2019

Xu ta kara da cewa, yawan jiragen dakon kaya na kasa da kasa, ya karu da kashi 22 cikin dari a shekara bisa na shekarar bara, zuwa 200,000, ciki har da jiragen fasinja 69,000 da aka mayar da su na jigilar kaya.

Jami’ar ta ce, a shekarar 2022, ana sa ran yawan jigilar kayayyaki cikin jirgin sama zai zarce tan miliyan 7.8 a shekarar 2022.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya