logo

HAUSA

Me Ake Nufi Da Aboki Na Zahiri? Kamar Sin Da Afrika

2022-01-10 21:10:04 CRI

"Kasar Kenya da nahiyar Afirka suna bukatar kawaye masu son yin hadin gwiwa da mu, don mu tabbatar da manufofinmu da burinmu." Wannan shi ne kalamin da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana, kwanakin baya lokacin da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya ziyarci kasar, inda ya bayyana yayin suka halarci bikin kammala aikin gina tashar mai ta Mombasa da kasar Sin ta gudanar da aikin ginawa. Shugaba Kenyatta ya yaba da goyon bayan da kasar Sin ke baiwa kasar Kenya, ya kuma kira kasar Sin a matsayin abokiya ta zahiri.

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya ziyarci kasashen Eritrea, da Kenya dake gabashin Afirka da kuma Comoros dake kudancin Afirka daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Janairu. Wannan al'ada ce ta tsawon shekaru 32 ta diflomasiyya ta kasar Sin, inda ministocin harkokin wajen kasar Sin suka kai ziyara nahiyar Afirka, don ziyarar farko a kowace sabuwar shekara. Duk da kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar, kasar Sin ta ziyarci nahiyar Afirka kamar yadda ta tsara a shekarar bana, wanda ke nuna tushen zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka.

A halin yanzu, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a nahyar Afirka, ya zarce miliyan 10, kuma adadin wadanda aka yiwa allurar rigakafin bai kai kashi 10 cikin 100 ba a nahiyar. Fiye da wata guda da ya gabata, kasar Sin ta ba da sanarwar sake ba da karin wasu alluran rigakafin biliyan 1 ga nahiyar Afirka. Yanzu haka wasu kasashen Afirka sun karbi alluran rigakafin daga kasar Sin daya bayan daya. A yayin wannan ziyara da minista Wang Yi ya kai a nahiyar Afirka, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta baiwa kasar Kenya karin wasu alluran rigakafin miliyan 10, tare da tallafawa kasar Comoros, wajen cimma burinta na ganin ta yiwa dukkan ‘yan kasar allurar rigakafin a cikin wannan shekara.

Domin kara bunkasa hadin gwiwar sassan biyu, ziyarar kasar Sin tana kara bayyana akai-akai. Misali, Sin da Kenya sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa a fannin tattalin arzikin zamani, da zuba jari, da aikin gona. Bugu da kari, kasashen Eritrea da Sin sun daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashensu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kana kasar Eritrea ta tsara wataa taswirar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu

Akwai hanyoyin jiragen kasa sama da kilomita 10,000, da hanyoyi kusan kilomita 100,000, da gadoji kusan 1,000, da kimanin tashoshin jiragen ruwa 100, da asibitoci da makarantu da yawa. Sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka, na ci gaba da amfanar al’ummomin nahiyar Afirka. Haka kuma kasar Sin ba ta gindaya wani sharadi na siyasa ko tilasta musu wani abu a hadin gwiwarsu. Kuma wannan ita ce manufar hadin gwiwar Sin da Afirka. Wannan ne ma ya sa kasar Sin a kullum take tafe da tsarin na abokantaka da amincewa da juna a nahiyar Afirka. Don haka, babu wani abin da zai lalata hadin gwiwar Sin da Afirka har abada.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya