logo

HAUSA

Nunawa ‘Yan Ta’adda Gata Shi Ne Keta Hakkin Bil Adama

2022-01-11 15:44:33 CMG

Nunawa ‘Yan Ta’adda Gata Shi Ne Keta Hakkin Bil Adama_fororder_taaddanci-0

Farkon duk sabuwar shekara, lokaci ne na gudanar da bukukuwa da jin dadi. Amma mutanen jihar Zamfara ta tarayyar Najeriya, sun tsunduma cikin yanayi na bakin ciki da zaman dar-dar, ganin yadda hare-haren da ‘yan fashin daji suka kaddamar ya haddasa mutuwar mutane fiye da 200, tare da raba mutane fiye da dubu 10 da muhallansu.

An ce, ‘yan fashin sun kaddamar da hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya ga sojojin Najeriya, bisa hari daga sama da sojojin suka yi kan maboyansu. Gaskiya ‘yan fashin sun wuce gona da iri, abun da ya sa mutanen duniya matukar takaici. Sai dai wadannan ‘yan fasahin daji, da gwamnatin Najeriya ta bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, su da dakarun kungiyar Boko Haram, sun shafe tsawon lokaci suna aikace-aikacen ta’addanci, da yake-yake a arewacin Najeriya.

Nunawa ‘Yan Ta’adda Gata Shi Ne Keta Hakkin Bil Adama_fororder_taaddanci-1

Makamantan wadannan ‘yan ta’adda sun ta da zaune-tsaye a kasar Khazakstan a kwanakin baya, inda suka yi amfani da zanga-zangar da aka gudanar a kasar, wajen kai hare-hare kan hukumomin kasar, da kwatar makamai, da kisan ‘yan sanda, tare da niyyar gudanar da juyin mulki a kasar. Sai dai yanayin bai ci gaba da lalacewa ba, bayan da hukumar tsaro da Khzakstan ta halarta ta CSTO, ta tura sojojin wanzar da zaman lafiya zuwa kasar, sa’an nan kasar Sin da sauran makwabtan kasar Khzakstan, su ma suka nuna goyon baya ga kasar.

Yanayin da kasar Khzakstan da sauran yankunan tsakiyar Asiya ke ciki, ya yi kama da na wasu yankunan dake yammacin Afirka, inda aka dade ana fama da masu tsattsauran ra’ayi, da ‘yan aware, da ‘yan ta’adda, wadanda suke ta kokarin haifar da barna a wuraren. Abun da ya kamata a yi, shi ne a murkushe su ba tare da waswasi ba.

Nunawa ‘Yan Ta’adda Gata Shi Ne Keta Hakkin Bil Adama_fororder_taaddanci-2

Yadda shugabannin kasar Khzakstan ke tsayawa kan matsayinsu na kare kasa daga ‘yan ta’adda, da yadda kungiyar tsaro ta CSTO ta mayar da martani cikin sauri, da goyon bayan da makwabtan kasar Khzakstan suka nuna mata, dukkansu sun nuna wani madaidaicin ra’ayin da ya kamata a samu, yayin da ake fuskantar aikace-aikacen ta’addanci.

Sai dai ya kamata mu lura da ra’ayin da kasar Amurka ta nuna, game da rikicin da aka samu a kasar Kazakhstan, inda Antony Blinken, sakataren harkokin wajen kasar, ya yi jawabi ga ‘yan kasar Kazakhstan cewa, “ Idan an bar mutanen kasar Rasha cikin gida, to, da kyar za a kore su.” Ma’ana wato bai kamata ba, a yarda sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar CSTO su shiga cikin kasar Kazakhstan. Sai dai kuma mene ne shawarar da kasar Amurka ta ba mutanen da suke fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda? Su mika wuya don a kashe su kawai?

Nunawa ‘Yan Ta’adda Gata Shi Ne Keta Hakkin Bil Adama_fororder_taaddanci-3

Sinawa ma sun san al’adar kasar Amurka da wasu kasashe na yammacin duniya, ta nuna fuskoki biyu game da batun dakile ta’addanci. Saboda jihar Xinjiang ta kasar Sin, wadda ta zama a dab da kasar Kazakhstan, ita ma ta sha jin radadin masu tsattsauran ra’ayi, da masu niyyar balle kasa, gami da ‘yan ta’adda, amma wasu mutane na kasashen yamma sun ga maciji kwance, suna bugun darari, inda suke kokarin mai da ‘yan ta’adda a matsayin “masu fafutukar neman ‘yanci”, da kallon matakin magance ballewar kasa a matsayin “keta hakkin dan Adam”. Wadannan mutane na ta’ammali da tasirin kafofin yada labaru na kasashen yamma, wajen yada karairayi a duniya, don neman bata sunan kasar Sin, da ta da rikici a kasar. Don cimma wannan buri, za su iya yarda da ‘yan ta’adda su kashe mutanen da ba su san hawa ba balle ma sauka.

Ya kamata mu tunatar da wadannan mutane cewa, yi wa ‘yan ta’adda gata shi ne ainihin keta hakkin bil Adama. Bari mu duba yanayi mai ban tausayi da dimbin mutanen dake jihar Zamfara suke ciki. Ko da yake sojojin Najeriya sun dade suna kokarin dakile ta’addanci, amma ‘yan ta’adda na ci gaba da ta da zaune tsaye a kasar. Idan aka bar su su gudanar da aikace-aikacensu yadda suka ga dama, to, mawuyacin halin da za a iya shiga ciki zai wuce tunanin mutum. Saboda haka, bai kamata a yi hakuri da duk wasu aikace-aikace, ko kuma zance na yiwa ‘yan ta’adda gata ba. (Bello Wang)

Bello