logo

HAUSA

Sin: Amurka ta sha yada jita-jita da batanci don dakile ci gaban kasar Sin

2022-01-11 20:23:04 CRI

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a taron manema labaru da aka saba yi Talatar nan cewa, zargin wai "kisan kare dangi" da laifin take hakkin bil-Adama a jihar Xinjiang, karya ce da wasu mutane a Amurka suka kirkira. Amurka ta sha yada jita-jita da batanci, da nufin bata sunan kasar Sin da kuma neman hana ci gaban Sin, amma makircinsu ba zai yi nasara ba. Kasar Sin za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka wajaba don kare ikon mallakar kasa, da martabarta, da hakki da ma moriyarta.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya