logo

HAUSA

Sin: Ya kamata Amurka ta gaggauta rufe gidajen yarinta na sirri dake sassan duniya

2022-01-12 20:01:07 CRI

Ranar 11 ga watan Janairu ne, ake cika shekaru 20 da kafa gidan yarin Guantanamo. Da yake amsa tambayoyi yayin taron manema labarai da aka saba yi Larabar nan. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, gidan yarin Guantanamo, wani shafi ne mai duhu a tarihin kare hakkin bil-Adama a duniya, kuma ya kamata Amurka ta gaggauta rufe gidan yarin na Guantanamo da ma dukkan gidajen yarinta na sirri a fadin duniya.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya