logo

HAUSA

Iran ta ce an samu raguwar cece-ku-ce a tattaunawar Vienna

2022-01-09 16:47:49 CRI

Babban jami’i mai shiga tsakani kan batun nukiliyar kasar Iran, Ali Bagheri Kani, ya bayyana a ranar Asabar cewa, yawan cece-ku-ce, ko kuma abin da ake kira kace-nace, suna raguwa a tattaunawar dake gudana a birnin Vienna, hedkwatar kasar Austria, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ba da rahoton.

Ali Bagheri Kani ya yi wannan tsokaci ne a karshen tattaunawar tsakanin wakilan kasar Iran da sauran bangarorin dake shafar yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015, gabanin fita daga otel din Coburg dake Vienna, inda ake ci gaba da gudanar da tattaunawa kan shirin nukiliyar Tehran.

Rahotanni sun ce, mai shiga tsakanin na Iran ya fadawa ‘yan jaridu cewa tattaunawar tana gudana kuma tana kara samun ci gaba.

Iran da sauran muhimman bangarorin biyar dake shafar yarjejeniyar nukiliyar Iran da suka hada da Sin, Rasha, Birtaniya, Faransa da Jamus, sun sha gudanar da tattaunawa a zagaye da dama a Vienna, yayin da Amurka a fakaice take shiga tattaunawar, da nufin farfado da yarjejeniyar, wacce Washington ta fice a shekarar 2018 karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.(Ahmad)

Ahmad