logo

HAUSA

Sin: Yawan Musayar Kudaden Da Ta Adana Ya Karu A Watan Disamba

2022-01-09 16:31:29 CRI

Alkaluman da mahukuntan kasar Sin suka fidda a Juma’ar da ta gabata sun nuna cewa, yawan musayar kudaden da kasar Sin ta adana ya karu a watan Disamban shekarar 2021 yayin da farashin darajar dalar Amurka ya fadi idan an kwatanta ta da sauran manyan kudade na duniya, hakan da ya sa darajar kaddarorin kasar Sin wadanda ba su shafi dalar Amurka ba ta karu.

Yawan musayar kudaden da kasar Sin ta adana ya kai dalar Amurka triliyan 3.2502 ya zuwa karshen watan Disamban shekarar 2021, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 27.78, ko kuma kaso 0.86 cikin 100, idan an kwatanta da na watan Nuwamba, kamar yadda hukumar kula da musayar kudaden da aka adana ta kasar Sin wato SAFE ta bayyana.

Da take tsokaci game da alkaluman, mataimakiyar shugaban hukumar SAFE, Wang Chunying ta ce, kasuwar musayar kudaden da kasar Sin ta adana tana ci gaba da samun tagomashi, inda take da karfi da kuma gudanar da ciniki bisa tsari mafi dacewa.

Wang ta danganta karuwar darajar kaddarorin kasar Sin wadanda ba su shafi dalar Amurka ba, bisa wasu manyan dalilai, ciki har da batun annobar cutar numfashi ta COVID-19, da muhimman manufofin dake shafar kudade da manyan kasashe suka aiwatar da su, lamarin da ya yi sanadiyyar karyewar darajar dalar Amurka.

A cewar madam Wang, ko da yake, akwai rashin tabbas a kasuwar hada-hadar kudi ta kasa da kasa, amma duk da hakan kwararan matakan tattalin arziki da kasar Sin take dauka da manyan tubalan da kasar ta kafa na dogon lokaci, sun taimaka wajen tabbatar da daidaito a yawan musayar kudaden da Sin ta adana.(Ahmad)

Ahmad