logo

HAUSA

Darasi Da Xi Jinping Ya Koyar Wa Manyan Jami’an JKS

2022-01-10 20:44:50 CRI

A ranar 11 ga watan Janairun shekarar 2021, Xi Jinping ya halaci bikin kaddamar da taron kara wa juna sani kan koyon ruhin cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na karo na 19 na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka shiryawa manyan jami’an lardunan kasar a kwalejin tsakiya na JKS, inda ya jaddada cewa, wajibi ne a yi nazari kan sabon tunanin raya kasa, a gaggauta kafa tsarin raya kasa, da kokarin raya kasar ta Sin a yayin da ake aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na raya kasar Sin karo na 14, ta yadda za a kaddamar da aikin raya kasar Sin ta zamani mai bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni yadda ya kamata.

Tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18 na shekarar 2012, ban da shekarar 2020, lokacin da aka samu barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, a ko wane farkon shekara, Xi Jinping, a matsayinsa na babban shugaban JKS, ya koyar da manyan jami’an JKS darasi, lamarin da ake ganin cewa, za a kara sanin manufar JKS dangane da mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa a sabuwar shekara.

A shekarar 2021, cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiya na karo na 19 yana da matukar muhimmanci a tarihi, wanda aka gudanar da shi a daidai lokacin da aka cika shekaru 100 da kafa JKS. A yayin taron, an zartas da kuduri dangane da muhimman nasarorin da JKS da ma kasar Sin suka samu, bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, manyan sauye-sauye da aka samu da gabatar da bukatar cimma manufar kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani da wadata, da bin tsarin demokuradiyya, wayin kai da jituwa nan da shekarar 2049 wato yayin da za a cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Yadda za a aiwatar da ruhin kudurin yadda ya kamata, ya zama wani muhimman aikin siyasa na JKS a halin yanzu da ma nan gaba. Kamar yadda Xi Jinping ya fada a yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, yin koyi da tarihi zai ilmantar da jama’a game da makomar da ake fatan samu a nan gaba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan