logo

HAUSA

Yadda shugaba Xi Jinping ke kokarin gudanar da harkokin diflomasiyya a shekara ta 2021

2022-01-03 20:39:30 CRI

Yadda shugaba Xi Jinping ke kokarin gudanar da harkokin diflomasiyya a shekara ta 2021_fororder_1

A bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci wasu muhimman harkokin diflomasiyya guda 40 ta kafar bidiyo, ya kuma zanta da shugabannin kasa da kasa, da manyan jami’an kungiyoyin duniya ta wayar tarho sau 79, kana sama da sau 100, ya gabatar da jawabi ko aikawa da sako ta kafar bidiyo.

A bara, shugaba Xi ya tsaya haikan kan manufar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, inda a karo da dama, ya jaddada cewa ya dace a kiyaye, gami da aiwatar da ainihin ra’ayin kasancewar bangarori da dama a duniya, da zummar yin kira a karfafa hadin-gwiwa da samar da ci gaba tare.

Har wa yau, a bara, shugaba Xi ya halarci taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, domin habaka hanyoyin hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

A ranar 21 ga watan Satumbar bara, a yayin muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76, Xi ya bullo da shawarar samar da ci gaban duk duniya karo na farko, a wani kokari na ciyar da duniya gaba zuwa sabon mataki.

Daga baya, a ranar 15 ga watan Disambar bara, shugaba Xi ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta kafar bidiyo, inda bangarorin biyu suka bayyana babbar aniyarsu, ta haduwa da juna ido da ido, a yayin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a Beijing, da nunawa duk duniya sakon inganta hadin-gwiwa, don fuskantar makoma mai haske. (Murtala Zhang)