logo

HAUSA

Jawabin Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Na Murnar Sabuwar Shekara

2021-12-31 21:17:28 CRI

 

Jawabin Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Na Murnar Sabuwar Shekara_fororder_00e93901213fb80e35e30ef618248727b83894db

A jajibirin sabuwar shekara ta 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara, ta babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da kuma yanar gizo. Yanzu ga cikakken jawabinsa da Bello Wang ya karanto muku:

 

Jama’a, barkanku da war haka, yayin da shekarar 2022 ke karatowa, ina mika muku gaisuwa da fatan alheri daga nan birnin Beijing!

Shekarar 2021 da aka ga karshenta tana da ma’ana ta musamman, saboda mun ga yadda wasu abubuwa masu ma’ana da suka faru a tarihin kasar Sin, da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulkin kasar. Yanzu haka muna kokarin cimma burinmu na gina al’umma mai walwala, da raya kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu. Yanzu haka mun kama hanyar cimma dukkan burikanmu na raya kasa, don tababtar da ci gaban al’umma.

Tun daga farkon shekarar 2021, har zuwa karshenta, jama’ar kasarmu suna ta hidima a cikin gonaki, da kamfanoni, da ungwanni, da makarantu, da asibitoci, da sansanonin soja, da cibiyoyin nazarin kimiya da fasaha. A kokarin samar da gudunmawa, da cimma dimbin nasarori, a wannan shekara mun ga yadda kasar Sin take kara samun ci gaba, ta hanyar jajircewa. Jama’ar kasar suna da kokari. Ana ta samun ci gaban harkoki a fannoni daban daban. Kana ana kokarin gadon fasahohi na wasu sana’o’i.

A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2021, mun shirya gagarumin bikin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A lokacin, na kalli yadda aka gudanar da bikin daga saman ginin Tian-An-Men. Abun da na gani ya burge ni sosai, kuma ya sa ni tunawa da tarihin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da yadda ta yi kokarin jagorantar dubun-dubatar jama’ar kasar Sin, wajen haye wahalhalu, da fuskantar dimbin matsaloli kafin ta kai ga cimma nasarori, da zama wata babbar jam’iyyar siyasa mai muhimmanci. Kar mu manta da burin da muka sanya a gaba tun da farko, ta yadda za mu iya cimma shi kamar yadda ake bukata. Dole ne mu yi matukar kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanmu, ta yadda za mu cancanci matsayinmu na tarihi da zamani, a idanun jama’a.

A yayin cikakken taro na 6 na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 19, da ya gudana a shekarar 2021, an zartas da kundin kuduri na 3 a cikin tarihin jam’iyyar. Dukkan nasarorin da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu cikin shekaru 100 da suka wuce, sun sa mu alfahari, kana dukkan fasahohin da aka samu sun zame muhimmin darasi. Na taba ambatar maganar da Mista Huang Yanpei da marigayi shugaban kasar Sin Mao Zedong suka fada game da al’adar tarihin dan Adam, don nuna cewa, dole ne mu yi kokarin gyara kurakuranmu don tabbatar da ci gaban harkokinmu a ko da yaushe. Nemen tabbatar da farfadowa da ci gaban al’ummar kasar Sin, ba aiki ne mai sauki ba, kuma wannan burin ba zai cika cikin kwana daya ba. Saboda haka ya kamata mu yi kokarin nuna hangen nesa, da hakuri, da jajircewa, da tunawa da matsalolin da ake iya fuskanta, sa’an nan a tsara manufofi masu dacewa, da gudanar da ayyuka a matakai daban daban yadda ya kamata.

Ya dace babbar kasa ta dauki nauyi mai yawa a duniya, kuma harkokin kasa harkokin al’ummun kasa ne, a don haka na kan samu sakamako bayan da na ziyarci da kuma yin nazari a wurare daban daban, inda kullum na kan tambayi mazauna wuraren a gidajensu, game da irin matsalolin da suke fuskanta, kuma ba zan manta da abubuwan da suka gaya mini ba.

Kana a ko da yaushe ina tunawa da damuwar al’ummun Sinawa, haka kuma ina kokari matuka, domin cimma burinsu. Hakika na girma a kauye, shi ya sa na san talauci sosai. Bayan kokarin da Sinawa suke yi daga zuriya zuwa zuriya, kawo yanzu mutane wadanda suka taba fama da talauci, sun riga sun samu isasshen abinci da sutura, tare kuma da samun damar shiga makaranta da gidajen kwana da inshorar lafiya. An lura cewa, tabbatar da matsakaicin wadata da kawar da talauci, yana daya daga cikin alkawuran da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi wa al’ummun kasar ta Sin, kana gudummawa ce da ta bai wa duniya baki daya. Nan gaba, za mu ci gaba da yin kokari domin kara kyautata rayuwar al’ummun kasarmu, a maimakon gamsuwa da sakamakon da muka samu yanzu.

A tarihin kasar Sin, al’ummun Sinawa suna sa ran ana tabbatar da tsaron Rawayen kogin, a cikin ’yan shekarun da suka gabata, na ziyarci jihohi tara da kogin ya ratsa, ko Rawayen kogi, ko kogin Yangtse, wadanda aka mayar da su matsayin mahaifiyar al’ummun Sinawa, ko tafkin Qinghai, ko kogin Yalizangbu, ko babban aikin sauya hanyar ruwa daga kudu zuwa arewa, ko “koren taswira” ta gandun daji na Saihanba, ko yawon giwaye daga kudu zuwa arewa a lardin Yunnan, da komawarsu inda suka fito, ko kaurar gadar jihar Tibet, duk wadannan sun nuna cewa, idan bil adama ya yi kokarin kiyaye muhalli, to tabbas za a cimma burin da aka sanya gaba.

A cikin shekarar da ta gabata, an kuma saurari muryar kasar Sin, da labaran kasar Sin, da suka burge mu, misali alkawarin matasa na “Kada jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta damu, za mu taka rawa kan aikin gina kasar”, da soyayya da aka bayyana ta “Muna kaunar kasar Sin”, da aikin binciken duniyar Mars na na’urar Zhurong, da aikin binciken duniyar rana na tauraron dan adama na Xihe, da aikin gina tashar binciken sararin samaniya ta Tianhe. Ban da haka, ’yan wasan kasar Sin suna yin takara a filin wasa domin samun lambobin yabo, daukacin al’ummun Sinawa suna kokari tare don dakile yaduwar cutar COVID-19, mutanen da suka sha wahalar masifa suna taimakawa juna domin sake gina gidajensu, sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin da ’yan sanda kwantar da tarzoma suna kara yin atisaye domin tabbatar da tsaron kasa, ana iya cewa, jarumai marasa adadi suna himmantu matuka, ta yadda za a ciyar da kasar Sin gaba yadda ya kamata a sabon zamanin da ake ciki.

Gwamnatin Sin na dora muhimmanci sosai kan wadata da zaman karkon yankin Hongkong da Macao. Hanya daya dilo da za a bi wajen tabbatar da hakan shi ne, tsayawa tsayin daka kan manufar “Kasa daya amma tsarin mulki iri biyu”. Dunkulewar kasa baki daya, shi ne burin al’ummar babban yanki da ma yankin Taiwan. Ina fatan dukkanin Sinawa za su hada kansu don cimma burin da muka sanya a gaba tare da samun ci gaba tare.

Lokacin da nake zantawa da shugabannin kasashen waje da na kungiyoyin kasa da kasa ta wayar tarho ko kafar bidiyo, sun sha jinjinawa gudunmawar da Sin take bayarwwa ga duniya wajen dakile cutar COVID-19. Ya zuwa yanzu, Sin ta samarwa kasashe ko kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120 alluran rigakafin biliyan 2. Hadin kai da taimakawa juna, ita ce hanya daya tilo da kasashen duniya za su yi wajen bude sabon babin tarihin samun kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.

Nan da wata daya da wani abu take tafe, za a bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da ajin nakasassu a nan kasar Sin. Burin gudanar da irin wannan gasa, shi ne baiwa karin mutane damar shiga wasannin kankara. Sin za ta yi iyakacin kokarinta don gabatar da wannan kasaitacciyar gasa. Sin ta shirya tsaf kan wannan gasa.

Ba da dadewa ba za a shiga sabuwar shekara. ’Yan saman jannatin Sin 3 suna gudanar da aikinsu a sararin samaniya, Sinawa dake gida da waje suna kokarin gudanar da ayyukansu, ban da wannan kuma jami’an ofisoshin jakadancin Sin dake ketare da ma’aikatan kamfanonin Sin dake ketare da dai sauransu, da daidaikun Sinawa dake aiki a ketare da kuma dalibai dake karo ilmi a ketare, suna dukufa kan matsayinsu, mutane da dama suna kokarin cimma burinsu. Ina nuna musu gaisuwa tare da fatan alheri.

Muna fatan samun ci gaba mai armashi da fatan alheri da samun bunkasuwar kasarmu da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a a nan gaba. (Bello/Jamila/Amina)