logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Ya Yi Jawabin Murnar Sabuwar Shekara

2021-12-31 20:28:59 CMG

Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Ya Yi Jawabin Murnar Sabuwar Shekara_fororder_xi

A jajibirin sabuwar shekara ta 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara, ta babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da kuma yanar gizo.

Shugban ya ce, shekarar 2021 da aka ga karshenta tana da ma’ana ta musamman, saboda an ga wasu abubuwa masu ma’ana a tarihi dangane da kasar ta Sin, da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulkin kasar. Yanzu haka ana kokarin cimma buri na gina al’umma mai walwala, da raya kasa ta kasar zamani mai bin tsarin gurguzu.

Ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, an saurari muryar kasar Sin, da labaran kasar Sin, masu burgewa, misali alkawarin matasa na “Kada jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta damu, za mu taka rawa kan aikin gina kasar”, da soyayya da aka bayyana ta “Muna kaunar kasar Sin”, da aikin binciken duniyar Mars na na’urar Zhurong, da aikin binciken duniyar wata na tauraron dan adama na Xihe, da aikin gina tashar binciken sararin samaniya ta Tianhe.

Ban da haka, shugaban ya ce ana sa ran samun ci gaba mai armashi nan gaba tare da nuna fatan alheri ga samun bunkasuwar kasa da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a nan gaba. (Bello/Jamila/Amina)

Bello Jamila Amina