logo

HAUSA

Dokar Amurka Ta “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Aikin Kwadago” Wata Babbar Karya Ce

2021-12-25 21:25:42 CRI

Dokar Amurka Ta “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Aikin Kwadago” Wata Babbar Karya Ce_fororder_新疆儿童

Ranar 25 ga wata, gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta shirya taron manema labaru dangane da dokar kasar Amurka da ta yiwa lakabin “haramta tilastawa al’ummar Uygur aikin kwadago”. A yayin taron, an karyata dokar ta Amurka mai cike da karairayi. Dalilin da ya sa Amurka ta sa hannu kan dokar shi ne bisa dokar da take aiwatarwa a gida, kana tana yunkurin dakile ci gaban kasar Sin bisa hujjar batun Xinjiang. Amma hakika dai babu wata kungiya ko wani mutum da ya tilas wa al’umma ‘yan kabilu daban daban su yi aiki a Xinjiang. Kowa da kowa na yin aiki ne cikin ‘yanci.

A yayin taron, Abudukeyoumujiang Reheman, wani mai girbin auduga a Xinjiang ya yi karin bayani kan yadda ya yi amfani da injuna wajen girbin auduga a gona mai fadin hekta 13.3 cikin yini guda a Xinjiang, inda a cewarsa, ya samu kudin shiga na kudin Sin RMB dubu 300, kwatankwacin dalar Amurka fiye da dubu 47. Har ila yau kuma, Abulaiti Wayiti, wani shehun malami a Jami’ar koyar da malamai ta Xinjiang ya bayyana cewa, a bana, dalibai 39 ne suka gama karatu a ajinsa, wadanda wasu 34 suka koma garinsu sun zama malamai a makarantun firamare da na midil, wasu 5 kuma sun zama ma’aikatan gwamnati.

Lalle batun yin aikin tilas a Xinjiang, wata babbar karya ce. Amurka ta sa hannu kan dokar bisa karyar da ta kirkiro, a yunkurin kwace ikon samun wadata ta hanyar yin aikin tukuru daga al’ummun Xinjiang, ta yadda za a tada kura a Xinjiang, da ma dakile ci gaban kasar Sin.

Ya zama tilas Amurka ta dakatar da kara gishiri kan batun Xinjiang, in ba haka ba, kasar Sin za ta mayar mata martani. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan