logo

HAUSA

Dokar Da Kasar Amurka Ta Zartas Ta Nuna Cewa Maganar Wai “Ana Danne ‘Yan Uygur” Karya Ce

2021-12-27 21:21:41 CMG

 

Dokar Da Kasar Amurka Ta Zartas Ta Nuna Cewa Maganar Wai “Ana Danne ‘Yan Uygur” Karya Ce_fororder_xinjiang-1

Kasar Amurka ta sake tsoma baki cikin harkar Xinjiang ta kasar Sin, inda ta gabatar da dokar wai “magance tilasta ‘yan Uygur aiki”. Sai dai wannan batun ya nuna cewa maganar “danne ‘yan kabilar Uygur a kasar Sin” karya ce kawai

Dalilin da ya sa na ce haka, shi ne domin duk lokacin da kasar Amurka ta nemi tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, ta hanyar fakewa da batun “kare adalci da hakkin dan Adam”, ta kan gabatar da wani dalili da ko kadan babu shi a zahiri.

Idan ba mu manta ba, a watan Fabrairun shekarar 2003, Colin Powell, tsohon sakatare harkokin wajen kasar Amurka, ya gabatar da wata kwalaba mai dauke da farin gari a wajen taron kwamitin sulhu na MDD, inda ya ce wai shaida ce kan yadda kasar Iraki ke kokarin samar da makamai masu guba. Daga baya, bisa wannan dalili ne, dakarun hadin gwiwa na kasashen Amurka da Birtaniya, suka kai hari kan kasar Iraki, da haddasa mutuwar dubun dubatar ‘yan kasar. Sai dai zuwa yanzu, kowa ya sani, abun da aka fada wai “ kasar Iraki ta mallaki makaman kare dangi” karya ce kawai.

Ban da wannan kuma, mun tuna da cewa, a watan Afrilun shekarar 2018, kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa, sun kai hari kan kasar Syria, bisa dalilin wai “gwamnatin Syria na yin amfani da haramtattun makamai masu guba”. Amma daga bisani an san shaidar da aka bayar wani hoton bidiyo ne da wata kungiyar al’umma ta hada. Wannan kungiya ta karbi kudi daga kasashen yammacin duniya, ta dauki wannan bidiyo na jabu, don nuna cewa, wai “gwamnatin Syria na kashe jama’a da ba su san hawa ba balle ma sauka, da makamai masu guba”.

Sa’an nan, a lokacin da wasu mutane ke bukatar taimako, ina kasar Amurka take? Misali, yanayin tsaro a arewacin Najeriya ya tsananta a wadannan shekaru, inda ake ta fama da hare-haren ta’addanci da sace mutane. Duk da haka, kasar Amurka ba ta taba nuna niyyar taimakawa kasar Najeriya ba, balle ma ta gabatar da wasu dokoki irin na tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya, ko kuma taimakawa Najeriya yakar ta’addanci.

Wasu abokaina sun nuna damuwa kan hakkin ‘yan kabilar Uygur na kasar Sin, amma a hakika suna yiwa lamarin bahaguwar fahimta. Don haka ina so in bayyana wasu abubuwa guda 3, don karyata kurakuran da aka nuna:

Na farko, tun shekaru 60 kafin haihuwar annabi Isa, yankin Xinjiang wani bangare ne na kasar Sin, wato daidai da zamanin daular Xi Han a lokacin. Tun daga lokacin har zuwa yanzu, Xinjiang wani wuri ne mai kunshe da kabilu daban daban, irinsu Uygur, da Khazak, da Tajik, da Mogolia, da Han, kana bai taba zama yanki dake karkashin mallakar ‘yan kabilar Uygur ba.

Na biyu, maganar wai “ jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana cin zarafin Musulmai” karya ce. Saboda jami’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulki a kasar, da gwamnatin kasar, suna kokarin kare ‘yancin jama’a na bin duk wani addinin da suke so. Idan jam’iyyar tana kin jinin addini, to, Hausawa da suke karatu da aiki a kasar Sin, cikinsu har da abokan aikina ‘yan kasar Najeriya da suke aiki tare da mu a cikin ofishin sashen Hausa na CRI, za su iya hakuri da batun? Kuna tsammanin za su iya shafe shekaru da yawa suna zama a kasar Sin, ba tare da ‘yanci a fannin bin addini ba? Za su yarda da hakan?

Na uku, shi ne maganar wai “gwamnatin kasar Sin na azabtar da ‘yan Uygur” karya ce, kuma jita-jita ce da wasu mutane ‘yan kabilar Uygur da suke kokarin balle yankin Xinjiang daga kasar Sin suka yada. Kamar dai yadda wasu ‘yan kabilar Igbo na Najeriya ke neman kafa “ jamhuriyar Biafra”, su mutane da suke neman janyo wa kasar Sin baraka, suna neman kafa wata “daular Islama ta Turkestan ta gabas”, wadanda MDD ta riga ta sanya sunayen wasu kungiyoyinsu cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Ko da yake maganar da aka fada dangane da Xinjiang karya ce maimakon hakikanin abun da ya faru, amma duk da haka, wannan batu na yin tasiri a duniya, har ma an yaudari mutane da yawa. Mene ne dalili? Saboda kasar Amurka da wasu kasashen dake yammacin duniya, suna goyon bayan wadannan masu neman raba kasa ‘yan kabilar Uygur, gami da ba su cikakken taimako ta fuskar yada jita-jita.

Amma me ya sa kasashen yammacin duniya ke son yin haka? Amsar ita ce, suna haka ne domin suna neman fakewa da batun Xinjiang, wajen hana abokiyar takararsu, wato kasar Sin, samun ci gaba.

Bayan da kasar Amurka ta gabatar da dokar “hana tilasta ‘yan Uygur aiki” a wannan karo, tabbas tana neman kakabawa kasar Sin takunkumi ne, don lalata yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da hana aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya.” Kana abun da kasashen yammacin duniya ke matukar son gani, shi ne jihar Xinjiang ta shiga tashin hankali, ta yadda za a yi wa tattalin arizki da zaman al’umma na kasar Sin zagon kasa. Ana son ganin faduwar karin wata kasar dake kan hanyar tasowa, don hana irin wadannan kasashe zama kan gaba a duniya.

Abokaina, za ku amince kasashen yamma, yayin da suke neman yin babakere a duniya? Ko kuma sabanin haka, ku nuna cikakken goyon baya ga kasar Sin, wadda a ko da yaushe take tare da sauran kasashe masu tasowa? Zabi ya rage gare ku. (Bello Wang)

Bello