logo

HAUSA

Jakadan Kasar Sin A Amurka: Ya Kamata A Yi Takara Tsakanin Sin Da Amurka Cikin Adalci

2021-12-25 17:33:58 CRI

Jakadan Kasar Sin A Amurka: Ya Kamata A Yi Takara Tsakanin Sin Da Amurka Cikin Adalci_fororder_sindaAmurka

Qin Gang, jakadan kasar Sin da ke kasar Amurka ya bayyana a kwanan baya cewa, hakika ana takara a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, amma takararsu ba irin ta cin moriya da faduwar wani ba ce. Ya kamata a yi takara a tsakanin kasashen 2 cikin adalci kuma yadda ya kamata. Takarar da ke tsakaninsu ta yi kama da tseren gudu, inda suka kara azama kan juna domin yin fintikau duka, maimakon yin wasan dambe. Kasashen 2 za su samu damar yin hadin gwiwa, ta haka za su kyautata karfin juna, tare da taimakawa juna.

Jakadan Sin ya kuma jaddada cewa, yanzu ba a yin takara cikin adalci a tsakanin kasashen Sin da Amurka. Amurka tana dakile ci gaban kasar Sin ne da sunan wai yin takara. Alal misali, ana cin zalin kamfanonin kasar Sin da dama ba tare da wani dalili ba. Amurka tana daukar wasu matakai ne da sunan tsaron kasa amma fiye da yadda take bukata. Amurka ta kuma ambaci wasu kamfanonin kasar Sin cikin jerin sunayen kamfanonin da aka sanya musu takunkumi, har ma wasu sun janye jiki daga kasuwar hada-hadar kudi ta Amurka. Jakadan kasar Sin ya nuna damuwa sosai kan irin wannan takara marar dacewa. Haka zalika Amurka tana yunkurin karfafa gwiwar kawayenta su hada hannu wajen mayar da kasar Sin saniyar ware a harkokin kasa da kasa. Yanzu kamfanonin kasar Sin suna fuskantar barazanar sanya musu takunkumi a kasar Amurka da ma tsarin kasa da kasa ta fannonin masana’antu, samar da kaya da kimiyya da fasaha. Ya zama tilas a kawo karshen irin wannan takara maras dacewa. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan