logo

HAUSA

Iran tayi Allah wadai da sabon takunkumin Amurka ta bayyanashi a matsayin tufka da warwara

2021-10-30 16:48:33 CMG

Iran tayi Allah wadai da sabon takunkumin Amurka ta bayyanashi a matsayin tufka da warwara_fororder_1030-Iran-Ahmad

Da yammacin jiya Juma’a kasar Iran tayi Allah wadai da takunkumai na baya bayan nan da Amurka ta sanya kan wasu daidaikun ‘yan kasar da cewa wata halayya ce dake nuna tufka da warwara.

A wani sharhin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya wallafa a shafin intanet na ma’aikatar ya nuna cewa, gwamnatin da ta bayyana aniyarta na sake komawa kan yarjejeniyar nukiliya, amma sai gashi tana cigaba da aiwatar da manufofin tsohon shugaban kasar Amurka President Donald na cigaba da sanya takunkumai, lamarin dake isar da sakon rashin tabbaci.

Ya kara da cewa, gwamantin Amurkar da ta gaji wacce ta shude, ta bayyana gazawarta a fili wajen kasa fahimtar hakikanin yadda Iran take.

Kakakin ya bayyana cewa, duk wani matsin lamba daga Amurka ba zai taba haifar da illa ko sauya manufofin gwamnatin Iran na tabbatar da tsaron kasarta da zaman lafiyar al’ummar kasar ba.

Tun da farko, kasar Amurka ta sanya takunkumai kan wasu kamfanoni da daidaikum jami’an kasar Iran da take dangantasu da shirin kasar na  mallakar jirage marasa matuka.(Ahmad)

Ahmad