logo

HAUSA

Shugaban Iran ya soki Amurka da lalata zaman lafiya a duniya

2021-09-02 10:36:36 cri

Jiya Laraba, a lokacin da yake magana kan halin da ake ciki a Afganistan a taron majalisar ministocin kasar Iran, shugaban kasar Ebrahim Raisi   ya ce, tarihi ya tabbatar sau da dama cewa, kasancewar Amurka a wasu kasashe da yankuna ba ya amfani ga tsaro, da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya.

Ebrahim Raisi ya ce, abubuwan da suka faru a Afganistan a cikin shekaru 20 da suka gabata, wata alama ce dake bayyana hakikanin take hakkin dan Adam a wannan zamanin na yau. Sannan idan aka duba yawan mata da yaran Afghanistan da aka kashe, ko kuma aka raunata a tsawon shekarun nan, za a iya gane cewa, yanzu ana fama da bala’i a Afghanistan. Kasancewar Amurka a kasashen waje ba ta taba haifar da tsaro ba, sai dai ta lalata tsaro, da kwanciyar hankali, da zaman lafiya. (Bilkisu)