logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Sin da Iran sun zanta ta wayar tarho

2021-11-07 16:48:08 CRI

Ranar 6 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna tare da takwaransa na kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ta wayar tarho.

A yayin tattaunawarsu, Wang Yi ya ce, kasashen Sin da Iran, abokai ne bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. Kasar Sin na son hada kai da Iran wajen ci gaba da kin amincewa da bin ra’ayi na kashin kai da yin danniya, tare da kiyaye ka’idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gida, a kokarin kare muradun bai daya na kasashe masu tasowa. Ministan harkokin wajen kasar Sin ya kara da cewa, kasar Sin ta yi maraba da kudurin Iran na komawa kan teburin shawarwarin maido da yarjejeniyar nukiliyar Iran a karshen wannan wata, lamarin da ya nuna yadda Iran ke kokarin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar. Kamata ya yi sassa daban daban su inganta taimakawa juna, su hada kai wajen ciyar da shawarwarin gaba bisa kyakkyawar manufa. Kasar Sin na marawa Iran baya da ta kara hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA, batun da zai samar da kyakkyawan yanayi wajen maido da shawarwarin.

A nasa bangaren, Hossein Amir-Abdollahian ya nuna cewa, sabuwar gwamnatin Iran za ta tsaya kan raya hadin gwiwar abota a tsakaninta da Sin. Iran ta yabawa matsayar kasar Sin da rawar da take takawa kan batun nukiliyar Iran. Iran za ta himmantu kan yin shawarwarin maido yarjejeniyar nukiliyar kasar, za ta kara tuntubar juna da taimakawa juna a tsakaninta da Sin. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan