logo

HAUSA

An tsare masu bore 5,800 a Kazakhstan

2022-01-09 20:56:54 CRI

Yau Lahadi ofishin yada labarai na shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya sanar da cewa, kimanin mutane 5,800 aka tsare a kasar Kazakhstan yayin da suke tsaka da yin bore, wadanda suka hada har da wasu baki ‘yan kasashen waje.

Kawo yanzu al’amurra sun daidaita a dukkan shiyyoyin kasar, yayin da aka samu farfadowar harkokin rayuwar yau da kullum a kasar.

Tokayev, ya bayyana a yayin wani taro cewa, gwamnatin ta sha alwashin maido da cikakkiyar doka da oda da tsaron al’umma a kasar da ke yankin tsakiyar Asiya.

Zanga-zanga ta barke ne bayan da aka samu mummunan tashin farashin man fetur cikin kwanaki da dama a kasar Kazakhstan, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka masu yawa da kuma jikkata wasu da dama.

A martanin da ya mayarwa masu zanga-zangar, shugaba Tokayev ya amince da rusa gwamnatin kasar a ranar Laraba, kuma ya bukaci taimakon kungiyar CSTO don kawo karshen tashin hankalin.

Shugaban kasar ya ayyana ranar 10 ga watan Janairu a matsayin ranar makoki a duk fadin kasar domin nuna juyayi ga mutanen da suka rasu.(Ahmad)

Ahmad