logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya tabbatar da matsayar kasar sa na adawa da duk wani mataki da ka iya daidaita Kazakhstan

2022-01-07 21:04:25 CRI

Shugaba Xi ya tabbatar da matsayar kasar sa na adawa da duk wani mataki da ka iya daidaita Kazakhstan_fororder_8ad4b31c8701a18b68eb8d2752b5a8012938feff

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya furta matsayar kasar sa, na adawa da duk wasu matakai da ka iya daidaita kasar Kazakhstan, da haifarwa kasar rashin tabbas ta fuskar tsaro, ko yi wa zaman lafiyar al’ummun kasar zagon kasa.

Cikin wani sakon murya da shugaba Xi ya gabatar ga takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, ya ce Sin na matukar adawa da duk wani yunkuri, na shigar sassan waje cikin harkokin Kazakhstan, da haifar da tashin hankali, ko rura wutar juyin juya hali a kasar.

Kaza lika ya yi tir da duk wani mataki daka iya gurgunta kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Kazakhstan, da gurgunta hadin gwiwar sassan biyu.   (Saminu)