logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a kai zuciya nesa a Kazakhstan yayin da zanga-zanga ke ta’azzara

2022-01-06 10:16:27 CRI

MDD ta yi kira da a kai zuciya nesa a Kazakhstan yayin da zanga-zanga ke ta’azzara_fororder_0106-Kazakhstan-Faeza

MDD ta ce tana bibiyar yanayin kasar Kazakhstan cike da damuwa, inda ta yi kira da a kai zuciya nesa.

Wata sanarwa da Stephane Dujarric, kakakin sakatare Janar na MDD ya fitar, ta ruwaito cewa, MDD na bibiyar yanayin da ake ciki a Kazakhstan cike da damuwa. Tana mai cewa abu ne mai muhimmanci dukkan wadanda ke da ruwa da tsaki cikin yanayin, su kai zuciya nesa, su kauracewa rikici da rungumar tattaunawa domin shawo kan dukkan matsaloli.

A cewar Stephane Dujarric, MDD na da ofis da ma’aikata a Kazakhstan, kuma kawo yanzu ba sa fuskantar wata barazanar tsaro.

Shugaban kasar Kassym-Jomart Tokayev, ya bayyana a jiya Laraba cewa, zai kara yin tsauri, yayin da yanayin kasar ke kara ta’azzara. Da farko a jiyan, ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa da amincewa murabus din gwamnatin kasar. (Fa’iza Mustapha)