logo

HAUSA

Shugaban Kazakhstan ya amince da rushe gwamnatin kasar

2022-01-05 20:31:35 CRI

Shugaban Kazakhstan ya amince da rushe gwamnatin kasar_fororder_38100c6c639942009fccaf5b8e606af6

Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na kasar Kazakhstan, ya amince da bukatar gwamnatin kasar mai ci ta yin murabus. Sai dai mambobin gwamnatin za su ci gaba da gudanar da ayyukan hukuma, har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.

Shugaba Tokayev, wanda ya amince da murabus din gwamnatin kasar a Larabar nan, ya kuma kaddamar da dokar ta baci a birnin Almaty, da kuma jihar Mangystau dake kudu maso yammacin kasar.

Fadar shugaban kasar ta ce, za a aiwatar da wasu matakai a tsawon wa’adin dokar ta bacin, ciki har da hana fitar dare tsakanin 11 na dare zuwa karfe 7 na safiyar ranekun dokar.  (Saminu)