logo

HAUSA

Mahukuntan Kazakhstan na iya shawo kan matsalar siyasa dake addabar kasar in ji ma’aikatar harkokin wajen Sin

2022-01-06 20:53:37 CRI

Mahukuntan Kazakhstan na iya shawo kan matsalar siyasa dake addabar kasar in ji ma’aikatar harkokin wajen Sin_fororder_42

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce mahukuntan kasar Kazakhstan na da ikon shawo kan matsalar siyasa dake addabar kasar su.

Wang, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, lokacin da aka yi masa tambaya game da zanga zanga dake wakana yanzu haka a Kazakhstan. Ana dai alakanta rikicin dake faruwa a kasar ne, da tashin farashin makamashin iskar gas.

Jami’in ya kara da cewa, "Abun da ke faruwa a baya bayan nan a Kazakhstan, harka ce ta cikin gidan Kazakhstan, kuma Sin na da yakinin cewa, mahukuntan kasar za su iya shawo kan matsalar yadda ya kamata”.   (Saminu)