logo

HAUSA

Iraqi ta karbi fursunonin IS 50 daga Syria

2022-01-09 16:41:58 CRI

A jiya Asabar kasar Iraqi ta bayyana cewa, dakarun tsaronta sun karbi fursunoni 50 ‘yan asalin kasar Iraqi wadanda mayakan kungiyar masu da’awar kafa daular musulunci ta IS ne da Syrian ta damke su.

An mika fursunonin ne ta hanyar kan iyakar Rabia dake lardin Nineveh a arewacin kasar Iraqi, karkashin jagorancin tawagar dakarun tsaron hadin gwiwa na Iraqi (JOC) da bangaren Syrian, kamar yadda ofishin yada labarai na JOC ta sanar.

Sanarwar ta ce, hukumar leken asiri da bincike ta ma’aikatar harkokin cikin gidan Iraqi ne ta karbi fursunonin domin daukar matakan shara’a a kansu.

Da ma dai Iraqin ta sha karbar rukunonin fursunoni ‘yan asalin kasar Iraqi daga bangaren Syrian a lokata da dama wadanda ke da alaka da mayakan IS da aka kama a Syria.

A shekarar 2014, mayakan IS sun yi ikirarin kafa dauloli dake karkashin ikonsu a yankunan kasashen Iraqi da Syria, sai dai an kashe dubban mambobin dake biyayya ga kungiyar IS tare da kama wasu bayan kwace ikon yankunan da kungiyar ke rike da su a Iraqi a shekarar 2017 daga bisani kuma kasar Syria.(Ahmad)

Ahmad