logo

HAUSA

Shugaba Xi ya taya Bashar al-Assad murnar lashe zaben shugabancin Syria

2021-06-01 13:39:09 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa takwaransa na Syria Bashar al-Assad, sakon taya murnar lashe zaben shugabancin kasar sa da ya gudana a kwanan baya.

Cikin sakon, Xi Jinping ya yi nunu da cewa, Sin na matukar goyon bayan Syria, a kokarin ta na kare ikon mulkin kai, da ‘yancin kare yankunan ta yadda ya kamata. Za ta kuma samar wa Syria tallafin abubuwan bukata na yaki da cutar COVID-19, da na farfadowar kasar, da inganta rayuwar ‘yan kasa, tare da daga matsayin hadin gwiwar su zuwa wani sabon mataki.  (Saminu)

Saminu