logo

HAUSA

Masana sun ce matakan Amurka sun keta hakkin dan adam tare da haifar da matsaloli a Syria

2021-07-04 16:04:45 CMG

Masana sun ce matakan Amurka sun keta hakkin dan adam tare da haifar da matsaloli a Syria_fororder_0704-Syria-Ahmad

Osama Danura, wani masanin harkokin siyasar kasar Syria ya ce, manufofin kasar Amurka a Syria a lokacin yakin basasar kasar cikin shekaru sama da 10 ya yi matukar haifar da munanan matsaloli game da yanayin jin kan bil adama kana ya take hakkokin dan adam na mutanen kasar Syria.

Danura, wanda ya kasance kwararren masanin kimiyyar siyasa, kuma tsohon mamba a tawagar wakilan da gwamnatin Syria ta tura don tattauna batun rikicin kasar a Geneva, ya bayyana a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a lokacin rikicin Syria, manufofin Amurka sun kara tsananta halin kuncin rayuwar da al’ummar kasar Syria ke fuskanta.

Ya ce, shisshigin da dakarun sojojin Amurka suka yi wa Syria a shekarar 2014, da nufin kawar da kungiyar masu da’awar kafa daular musulunci ta IS, sun kara haifar da mummunar barna da hasarar rayuka a kasar, ya kara da cewa, hare hare ta jiragen sama da Amurka ta kaddamar a arewaicn lardin Raqqa ya haifar da mummunar barna wajen lalata kayayyakin more rayuwa da kashe fararen hula marasa adadi.

Ya ce, abu mafi muni da Amurka ta yi shi ne, sanya takunkumi kan kasar Syria, wannan mataki ya kara tsananta mawuyacin halin da al’ummar kasar Syria ke fuskanta.(Ahmad)

Ahmad