logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a mayar da hankali kan halin da Amurka da Birtaniya suka jefa Syria a ciki

2021-07-07 11:39:24 CRI

Sin ta yi kira da a mayar da hankali kan halin da Amurka da Birtaniya suka jefa Syria a ciki_fororder_叙利亚

Wakilin Sin ya ce ya zama wajibi hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, ta mayar da hankali kan halin da Amurka da Birtaniya da sauran wasu kasashe suka jefa al’ummar Syria. Jam’in na Sin ya bayyana haka ne jiya, lokacin da yake jawabi ga taron tattauna batun Syria, a zama na 47 na hukumar dake gudana.

A cewarsa, a bana ake cika shekaru 10 da barkewar rikici a Syria. Kuma mafitar da ta dace da yanayin kasar ita ce maslaha a siyasance, yana mai cewa wannan hakki ne na al’ummar kasar, domin su tsara makomarsu ba tare da dogaro da wani ba. Ya ce Amurka da Birtaniya na da hannu dumu-dumu cikin yanayin da Syria ke ciki yanzu. Ya kara da cewa, Amurka da Birtaniya da sauran wasu kasashe sun kaddamar da hare-hare ta sama kan Syria, lamarin da ya rutsa da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, tare kuma da raba wasu da matsugunansu. Haka kuma sun yi gaban kansu wajen kakaba takunkumai masu tsanani kan kasar, wadanda suka kawo tsaiko ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da kokarinta na yaki da annobar COVID. Bugu da kari, ya ce kasashen ba su damu da hakkokin jama’a ba ko kadan, sai dai amfani da shi wajen nuna karfi da tsoma baki cikin harkokin da ba su shafe su ba da cin zali da shafawa sauran kasashe bakin fenti. (Fa’iza Mustapha)