logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a inganta agajin da ake kai wa ta iyakar Syria tare da dagewa kasar takunkumai

2021-07-10 17:00:04 CMG

Sin ta yi kira da a inganta agajin da ake kai wa ta iyakar Syria tare da dagewa kasar takunkumai_fororder_syria

Kasar Sin ta yi kira da inganta samar da agajin jin kai da ake kai wa ta iyakar Syria, tare da dage takunkuman da aka sanyawa kasar.

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun ne ya yi kiran, bayan kwamitin sulhu na majalisar ya amince da kudurin tsawaita shirin kai agaji daga iyakar kasar da watanni 12.

A cewar Zhang Jun, Sin na maraba da amincewa da tsawaitar shirin da daukacin mambobin kwamitin suka yi. Kana tana ba batun yanayin jin kai na Syria muhimmanci, tare da goyon bayan kasashen duniya da hukumomin MDD, wajen inganta kai kayayyakin agaji ga mutanen Syria karkashin ka’idojin majalisar.

Ya ce a ganin kasar Sin, kamata ya yi dukkan ayyukan jin kai a Syria, su kasance bisa martaba cikakken ‘yanci da yankunan kasar.

A cewarsa, shirin kai kayayyakin agaji ta iyaka, abu ne da aka tsara karkashin yanayi na musammam. Don haka, ya kamata a rika nazarinsa a kan kari da aiwatar da gyare-gyaren da suka danganci ingancinsa bisa la’akari da yanayin da ake ciki, tare da fatan sauya shi daga kai wa ta iyaka, ta yadda zai sa kayayyaki na bi ta cikin kasa. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza