Kasashen Sin da Australia na kokarin kyautata da bunkasa dangantakar dake tsakaninsu
2022-12-22 21:05:16 CMG Hausa
Jiya Laraba 21 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da gwamnan janar na Australia David Hurley, da firaministan kasar Anthony Albanese, suka taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Australia ta wayar tarho. A wannan rana kuma, ministocin harkokin wajen kasashen kasashen biyu, sun gudanar da taron tattaunawar diflomasiyya, da manyan tsare-tsare karo na shida tsakanin Sin da Australia a nan birnin Beijing, inda suka cimma matsaya da dama, kan kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu. Wannan shi ne sabon kokarin da kasashen Sin da Australia suka yi na kyautata da bunkasa dangantakar dake tsakaninsu.
Dukkanin sassan biyu wato Sin da Autralia, kasashe ne masu muhimmanci a yankin Asiya da tekun Pasifik. Amma, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa ga ingiza gasar manyan madafun iko da kasar Amurka ke yi, wasu 'yan siyasar Australia sun yi watsi da kyakkyawan tsarin samun moriyar juna da hadin gwiwar sada zumunci da kasar Sin, sun kuma bi Amurka wajen murkushe kasar Sin.
A watan Mayun bana, bayan da jam’iyyar Labour Party ta hau kan karagar mulkin sabuwar gwamnatin kasar Australia, ta nuna aniyarta ta inganta, da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Hakan ya samar da damar kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Har yanzu dai, dangantakar Sin da Australia tana fuskantar kalubale. Bisa irin yanayin da ake ciki, ya kamata bangarorin biyu su sake komawa kan ainihin burinsu, tare da daukar bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyyar su, a matsayin wata dama ta tabbatar da muhimman matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sa kaimi ga kyautata, da bunkasa dangantakar kasashen biyu. Dangantakar da ke tsakanin Sin da Australia mai inganci, ba wai kawai tana dacewa ne da babbar moriyar jama'ar kasashen biyu ba ne, har ma tana sa kaimi ga samar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da wadata a yankin Asiya da tekun Pasifik da ma duniya baki daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)