logo

HAUSA

Shahbaz Khan: Kasar Sin Ta Ba Da Babbar Gudummowa Wajen Kiyaye Abubuwan Tarihi Na Al’adu Da Na Halittu Na Duniya

2021-12-27 11:42:37 CRI

Shahbaz Khan: Kasar Sin Ta Ba Da Babbar Gudummowa Wajen Kiyaye Abubuwan Tarihi Na Al’adu Da Na Halittu Na Duniya_fororder_sin

Kwanan baya, wakilin hukumar ilmi, kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO a kasar Sin Shahbaz Khan ya ce, kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen kiyaye abubuwan tarihi na al’adu da na halittu na duniya, ta kuma ba da gudummawa wajen samun dawaumammen zaman lafiya da ci gaba a duniya. Khan ya yi fatan cewa, kasar Sin za ta yi musayar kyawawan fasahohinta da kasashe masu ruwa da tsaki, karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A shekarar 2021, an tanadi wani shirin kasar Sin mai lakabin “Quanzhou na kasar Sin: cibiyar kasuwanci da cinikayya ta duniya a teku a zamanin daulolin Song da Yuan”, cikin takardar sunayen abubuwan tarihi na kasa da kasa. Ta haka yawan abubuwan tarihi na kasa da kasa a Sin suka kai 56, kuma kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi samun abubuwan tarihi na al’adu da halittu na duniya.

A ganin Shahbaz Khan, akwai abubuwan tarihi na halittu masu yawa a kasar Sin. Haka zalika, kyawawan fasahohin kasar Sin, da kwararru masu ruwa da tsaki su ma suna taimakawa sauran kasashe wajen kiyaye abubuwan tarihi.

Jami’in MDD ya yi nuni da cewa, “Idan kasashen duniya ba sa bin manufar cudanyar sassa daban daban, to, ba za a warware munanan matsalolin da ake fuskanta yanzu ba. Alal misali, samun zaman lafiya, samun ci gaba mai dorewa, sauyin yanayi, da gazawa wajen samun wanzuwar halittu iri daban daban a duniya. Muna bukatar raya duniya mai ba da damar cudanyar sassa daban daban don warware matsalolin. Kasar Sin ta samu nasarar fitar da mutane miliyan 770 daga kangin talauci. Tana kuma taimakawa sauran kasashe karkashin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, lamarin da ya kasance hanya da ake bi wajen aiwatar da manufar cudanyar sassa daban daban.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan