logo

HAUSA

Jami’in MDD ya bukaci jami’an tsaron Sudan su mutunta zanga zangar lumana

2021-10-30 16:46:21 CMG

Jami’in MDD ya bukaci jami’an tsaron Sudan su mutunta zanga zangar lumana_fororder_1030-Sudan-Ahmad

Jiya Juma’a wani jami’in MDD ya bukaci jami’an tsaron kasar Sudan dasu mutunta hakkin masu zanga zangar lumana kwana guda gabanin soma wata zanga zangar da ake sa ran gudanarwa a ranar Asabar.

Volker Perthes, shugaban tawagar jami’an tallafawa shirin kafa gwamanati na MDD dake Sudan, UNITAMS, cikin wata sanarwa, ya bukaci jami’an tsaron Sudan su mutunta hakkin masu zanga zangar lumana kana su guji amfani da hanyoyin tayar da hankulla.

Sannan ya bukaci masu zanga zangar dasu gudanar cikin lumana, kana su guji tayar da rikici.

Jami’in MDD yayi kiran a bi dukkan matakan da zasu tabbatar da gina cikakkiyar tattaunawa a tsakanin dukkan bangarorin kasar domin cimma nasarar shirin maido da zaman lafiyar Sudan.(Ahmad)

Ahmad