logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a tsakaita bude wuta a fadan arewacin Somalia

2021-12-25 16:40:32 CRI

MDD ta yi kira da a tsakaita bude wuta a fadan arewacin Somalia_fororder_索马里

Babban jami’in kula da ayyukan ba da agaji na MDD a kasar Somalia ya yi kiran a tsakaita bude wuta a yankin Bossaso, birnin kasuwanci dake tashar ruwa a arewa maso gabashin kasar Somalia, an shafe kwanaki uku ana kazamin fada tsakanin mayakan dakarun tsaron dake gaba da juna.

Adam Abdelmoula, babban jami’in kula da ayyukan ba da agaji na MDD a kasar Somalia ya bayyana damuwa game da mawuyacin halin da yakin da ake gwabzawa zai haifar ga fararen hular yankin Bossaso dake jahar Puntland.

Ya nuna cewa, an ba da rahoton cewa, sama da rabin al’ummar birnin Bossaso sun kauracewa gidajensu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun rundunar tsaron jahar Puntland wato PSF ta yaki da ta’addanci wanda kasar Amurka ta horar da su, da kuma jami’an tsaron jahar dake biyayya ga shugaban jahar Puntland Saed Abdullahi Deni.

A cewar hukumomin samar da tallafin jin kai da mahukuntan wurin, kusan kashi 40 bisa 100 na ‘yan gudun hijira 70,000 dake zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira na Bossaso, sun sake yin kaura a karo na biyu.

Rikici wanda ya barke a ranar Talata, ya fuskanci kakkausar suka daga shugabannin kasar Somalia har da shugaban kasar Mohamed Farmajo.(Ahmad)

Ahmad