logo

HAUSA

Antonio Guterres: Nuna goyon baya ga ‘yan ci rani a halin yanzu ya fi muhimmanci sama da kowane lokaci

2021-12-19 16:58:55 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce nuna goyon baya ga bakin kasashen waje a halin yanzu ya fi kowane lokaci muhimmanci, kamar yadda ya bayyana a sakonsa na ranar bakin kasashen waje ta kasa da kasa, wacce ake murna a ranar 18 ga watan Disamban kowace shekara.

Jami’in ya kara da cewa, ba kawai ana bukatar nuna goyon baya ga bakin kasashen waje cikin gaggawa ba, har ma ana bukatar karin yin kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da kuma daukar matakan mafiya dacewa don tinkarar matsalar.

Guterres ya ce, a wannan rana, an lura da irin gudunmawar da bakin kasashen waje ke bayarwa ga dukkan sassan duniya ta fuskar yin gwagwarmaya a fannoni daban daban, wadanda suka hada da yaki da annobar COVID-19.

Sai dai kuma, ya ce bakin kasashen waje suna ci gaba da fuskantar yawaitar matsalolin nuna kyama, da rashin daidaito, da nuna musu bambanci, da wariyar launin fata da dai sauransu. Mata da ‘yan mata kuma suna fuskantar tsananin barazanar ci musu zarafi da karancin samun damar neman goyon baya.

Guterres ya ci gaba da cewa, yayin da iyakokin kasashe suka kasance a rufe, bakin kasashen waje da dama suna gararamba da rashin kudaden shiga da wurin zama, ba su samu damar sake komawa kasashensu ba, sun rabu da iyalai, ba su san makomar rayuwarsu ba.

Alkaluman MDD sun nuna cewa, an yi kiyasin mutane kusan miliyan 281 a matsayi ‘yan ci rani na kasa a kasa a shekarar 2020, wanda ya kai kashi 3.6 bisa 100 na yawan al’ummar duniya.(Ahmad)

Ahmad