logo

HAUSA

Jamhuriyar jama’ar kasar Sin za ta kira taron murnar cika shekaru 50 da dawo mata da halasatacciyar kujerar ta a MDD

2021-10-22 20:32:12 CRI

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a wani taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da aka dawo wa da Jamhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD.

A cikin shekaru 50 da suka gabata, kasar Sin ta kasance mai martaba kasancewar bangarori daban-daban, da tsarin kasa da kasa bisa jagorancin MDD, da tsarin kasa da kasa bisa dokokin kasa da kasa, da kuma muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a harkokin kasa da kasa. A cikin shekaru 50 da suka gabata, kasar Sin ta shiga cikin ayyukan MDD sosai, da kiyaye zaman lafiya a duniya, da inganta ci gaba tare, da ci gaba da fadada hadin gwiwa da MDD.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoba, Jamhuriyar jama’ar kasar Sin za ta shirya wani taro a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, don murnar cika shekaru 50 da dawo mata da halastacciyar kujerarta a MDD. Shugaba Xi Jinping zai halarci taron kuma zai gabatar da muhimmin jawabi. (Ibrahim)

Ibrahim